Sudan

An kashe shugaban ‘Yan tawayen Darfur

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur Reuters

Rahotanni daga Sudan sun ce dakarun kasar sun kashe shugaban ‘Yan tawayen yankin Darfur Ali Karbino wanda ke jagorantar hare haren akan Jami’an tsaron kasar. Gwamnan yankin arewacin Darfur Osman Kabir ne ya fitar da sanarwar kisan jagoran na ‘Yan tawayen kamar yadda Cibiyar yada labarai a kasar Sudan SMC ta ruwaito.

Talla

Sanarwar kuma tace an kashe jagoran ne tare da wasu manyan mabiyansa a wani samame da dakarun gwamnati suka kai a Al Guba yankin Kutum da ke cikin Jahar El Fasher.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.