Somalia

Somalia: Al Shabaab zata kai hare hare a cikin Azumi

Jami'an tsaro a kusa da inda Bom ya tashi a cikin wata mota a birnin Mogadishu
Jami'an tsaro a kusa da inda Bom ya tashi a cikin wata mota a birnin Mogadishu

Kungiyar Al Shabaab ta aiko da sakon gargadi akan zata kaddamar da sabbin hare hare a birnin Mogadishu a cikin watan Azumin Ramadan. A cikin wani sako na sauti, kwamandan kungiyar Sheik Ali Mohammed Hussein yace lokaci ya yi da zasu kaddamar da hare hare a Somalia.

Talla

Rahotanni a Somalia sun ce gwamnatin kasar ta girke Jami’an tsaro da dama dauke da makamai a sassan yankunan birnin Mogadishu saboda barazana daga Al Shabaab.

Kwamandan Mayakan Al Shabaab Sheik Ali Mohamed Hussein yace zasu tsaurara hare hare a watan Azumi saboda lokaci ne da ake yawaita bautar Ubangiji da yin Jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.