Nigeria

An kashe mutane akalla 50 a jihar Bornon Najeriya

Jami'an tsaron Najeriya na farautar Boko Haram
Jami'an tsaron Najeriya na farautar Boko Haram Ben Shemang / RFI

Bayanai daga jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya sun ce har zuwa safiyar yau litinin jami’an tsaro sun ci gaba da kirga hasarar rayuka da kuma ta dukiyoyi sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a wasu kauyuka da kuma coci-coci da dama a kusa da garin Chibok a jiya lahadi.

Talla

Rahotanni sun ce mutane da wasu ke cewa magoya bayan kungiyar Boko Haram ne, sun afka wa kauyuka dauke da manyan makamai, inda suka rika buda masu wuta, yayin da aka ce wasu daga cikin maharan sun shiga a cikin mujami’u a daidai lokacin da aka fara ibada.

Alkaluman da ba na hukuma ba ne, na nuni da cewa an kashe mutane fiye da hamsin a wadannan hare-hare na jiya lahadi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.