Isa ga babban shafi
Algeria

An yi wa Amurka barazanar hare hare a Algeria

Jami'an tsaro sun kewaye cibiyar Gas ta Amenas a kasar Algeria
Jami'an tsaro sun kewaye cibiyar Gas ta Amenas a kasar Algeria REUTERS/Louafi Larbi
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau | Abdoulkarim Ibrahim
Minti 1

Kasar Amurka ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar za a kai wa ofishin jakadancinta da ke birnin Algiers na kasar Algeria hari, kuma ta bukaci Jami’an diflomasiyarta a kasar su kauracewa Otel mallakin kasar Amurka a ranakun hutun samun ‘Yanci da za’a gudanar.

Talla

Wata jarida da ake bugawa a Algeria, ta jiyo wani babban jami’in ofishin jakadancin na cewa kasar na cewa suna daukar wannan barazana ta ta’addaci da mutukar muhimmanci.

Akwai wani hari da Mayakan Al Qaeda uska kai a wata cibiyar gas ta Amenas a 2013 inda suka yi garkuwa da ‘Yan kasashen waje 40 tare da kashe Amurkawa guda uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.