Masar

Sisi ya kara farashin Mai a Masar

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Egyptian Presidency/Handout via Reuters

Shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi ya kara Farashin mai bayan datse tallafi da al’ummar kasar ke samun rahusa a wani mataki na kokarin farfado da tattalin arzikin kasar da ya tabarbare tsawon shekaru uku da aka kwashe ana rikici a kasar.

Talla

Ana ganin wannan matakin na iya janyo wa Al Sisi bakin jini wanda aka zaba a watan Mayu.

Yanzu haka shugaban wanda ya hambarar da gwamnatin Morsi ta ‘Yan uwa Musulmi yana kokarin datse kasafin kudin kasar don daukar matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

Gwamnatin Masar dai tana ware kusan kashi 30 na kasafin kudinta akan tallafin Mai da  abinci ga al’ummar kasar inda kashi 40 talakawa ne.

Amma Firaministan kasar ya shaidawa Misrawa a kafar telebijin cewa karin farashin Man ba zai shafi farashin kayyakin abinci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.