Nigeria

Mata fiye da sittin sun tsere daga hannun Boko Haram

Masu fafutukar ceto 'yan matan Chibok daga Boko Haram
Masu fafutukar ceto 'yan matan Chibok daga Boko Haram REUTERS/Afolabi Sotunde

Majiyoyin tsaro a jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya, sun bayyana cewa mata 63 daga cikin 68 da aka sace cikin watan yunin da ya gabata, sun tsere daga hannun wadanda suka sace su.

Talla

Rahotanni sun ce matan, sun tsere daga hannun maharansu ne a daidai lokacin da maharan suka tafi domin kai hari a wani barikin soja da ke garin Damboa a jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

A cikin watan Yunin da ya gabata ne dai ‘yan bindiga da ake zaton magoya bayan Boko Haram ne suka sace matan su 68 a garin Kummabza, to sai dai har yanzu ana kyautata zaton cewa akwai sauran matan wannan kauye a hannun ‘yan bindiga, yayin da har yanzu ake ci gaba da yin garkuwa da wasu ‘yan matan fiye da 200 da aka sace a garin Chibok.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.