Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Kungiyar Seleka ta ce bata da Hannu ga kisan jama’a

online.wsj.com

Rahotannin da ke fitowa daga Jamhuriyar Africa ta tsakiya na nuna cewa sabon rikici ya barke a garin Bambari, tsakanin mabiya Addinai, Sai dai kakakin ‘yan kungiyar Seleka Kanal Narkoyo ya sheidawa Rediyo Faransa cewa babu hanu ‘yan kungiyar a wanan sabon rikici

Talla

Wannan rikicin ne ya sa Ministan Tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian, da ya kai ziyara a kasar ta Jamhuriyar Africa ta Tsakiya, ya soke ziyarar da ya shirya kai wa yankin Bambari.

Kakakin yan kungiyar Seleka Kanal Narkoyo ya sheida wa Rediyo Faransa da cewa babu hanu yan Seleka a wanan sabon rikici.

Yace matasan Unguwa ne suka nuna fushinsu bayan da ‘yan kungiyar Antibalak suka kashe wani matashin Uguwa.

Wadanan matasa a cewarsa, sun kai wa ‘yan kungiyar Antibalaka hari ne a wata majami’a da ke a garin na Bambari, kuma yukunri wadanan matasa na tattare da hatsari gani yadda suka manta da Dakarun Sangaris dama ‘yan kungiyar Seleka, sabili da haka ma ‘yan kungiyar ta Seleka suka dau nauyi kai masu dauki domin kare lafiyar wadanan matasa dama mutane da ke samun mafaka a wanan majami’a.

Ku san da cewa makamai na yawo ne a Uguwani da dama a garin na Bambari.

Yan kungiyar Seleka sun yi nasarar korar wadanan matasa, ‘yan seleka, amma ba su da Hannu a wanan rikicin na garin Bambari, kuma ya dace mu yabawa ‘yan kungiyar Seleka da ke garin na Bambari, domin sun tabbatar da tsaro har wayewar garin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.