Afrika ta Tsakiya

Ana zaman makoki a Afrika ta tsakiya

Sojojin kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya suna sauraren bahasi daga shugaba Samba-Panza a Bangui
Sojojin kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya suna sauraren bahasi daga shugaba Samba-Panza a Bangui AFP PHOTO/ ISSOUF SANOGO

Al’ummar kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya sun fara zaman makoki na kwanaki uku bayan wani kazamin hari da ‘Yan bindiga suka kai a wata Mujami’a inda suka kashe mutane 26 da suke kwana a ciki saboda rikicin kasar da ya raba su da gidajensu.

Talla

Shugaba Catherine Samba Panza ta yi Allah wadai da harin tare da zargin Mayakan sa-kai, anti balaka da Seleka.

Tun a ranar Alhamis ne aka fara zaman makoki a kasar domin juyayin kisan mutanen da aka kashe a ranar Litinin a yankin Bambari.

Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar sun bude wa mutanen wuta ne kuma Kimanin mutane 35 suka jikkata.

Tun a watan Maris din bara ne kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici bayan Michel Djotodia ya jagoranci Mayakan Seleka suka kifar da gwamnarin Francois Bozize.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.