Libya

Mayakan Libya sun gwabza fada a Tripoli

Hayaki ya turmuke sama a birnin Tripoli a lokacin da ake musayar wuta tsakanin Mayakan libya a kusa da tashar jirgin sama.
Hayaki ya turmuke sama a birnin Tripoli a lokacin da ake musayar wuta tsakanin Mayakan libya a kusa da tashar jirgin sama. REUTERS/ Hani Amara

Rahotanni daga Libya sun ce an yi mummunar artabu tsakanin kungiyoyin ‘Yan tawayen kasar guda biyu, lamarin da ya sa aka rufe tashar jirgin sama a Tripoli. Ma’aikatar Lafiya ta tabbatar da mutuwar mutane 6 a musayar wuta da aka yi tsakanin bangaoririn Mayakan guda biyu.

Talla

Kimanin Mutane 25 ne suka jikkata, amma babu wani cikakken bayani ko akwai fararen hula cikin wadanda aka kashe.

Wakilin Kamfanin dillacin Labaran Faransa yace mutanen birnin Tripoli sun ji karar fashewa da harbin bindiga, tare da harbo roka a harabar tashar jirgin sama.

Rahotanni sun ce Ministan harakokin wajen Libya ya nufi Tunisia domin tattauna yadda kasar zata taimakawa Libya a kawo karshen rikicin da ke addabarta

An yi wannan artabun ne dai tsakanin Mayakan garin Zintan da suka taimaka aka kifar da gwamnatin Marigayi Kanal Ghaddafi  da wasu ‘Yan bindiga da ke yakin neman kafa gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.