Afrika ta Kudu

Ana bikin ranar Mandela ta duniya

Yau juma’a ita ce ranar Mandela ta duniya, karo na farko tun bayan mutuwarsa dan gwagwarmaya wanda ya rasu a ranar 5 ga watan Disambar bara yana da shekaru 96 a duniya. An kebe wannan rana ta 18 ga watan Yuli ne a matsayin ranar Mandela, ranar da aka cika shekaru 67 da soma gudanar da gwagwarmayarsa wadda ta kai ga samar wa al’ummar Afirka ta Kudu ‘yanci.

Marigayi Nelson Mandela Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu.
Marigayi Nelson Mandela Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu. © AFP/Louise Gubb
Talla

Masoyan Mandela a fadin duniya ne ke gudanar da bikin domin tuna shi da kuma rawar da ya taka ta kawo karshen wariya a Afrika ta kudu.

A karon farko bayan mutuwarsa, dimbin mutanen duniya zasu gudanar da bikin karrama tsohon shugaban na Afrika ta kudu a biranen Paris da New York da London da Glasgow da kuma birnin Beijing na China.

Mandela ya kwashe shekaru 27 a gidan yari a lokacin da ya ke gwagwarmayar adawa da fararen fata, kuma bayan ya fito daga gidan yari ya bayyana yafewa Turawan da suka kargame shi tare da jagorantar zabe a Afrika ta kudu.

Shugaba Jacob Zuma ya jagoranci al’ummar kasar Afrika ta kudu da tsintsiya domin share kasar don karrama Mandela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI