Bakonmu a Yau

Bakonmu a yau Dr Abarshi Magalma

Sauti 03:18

Shugaba Francois Hollande na kasar Faransa zai isa birnin Yamai na jamhuriyar Nijar domin gudanar da ziyarar aiki ta tsawon sa’o’i 24, wato daya daga cikin kasashe 3 na Afirka da shugaban ya shirya kai wa ziyara a wannan mako

Talla

Batutuwan tsaro da kuma na tattalin arziki, na daga cikin muhimman abubuwan da ke tafe da shugaban na Faransa. A ranar alhamis dai Hollande ya kasance ne a kasar Cote D’Ivoire, inda ya gana da shugaba Alassan Ouattara da kuma wakilan ‘yan adawa.
Hollande ya yaba da irin ci gaba da kasar ta Ivory Coast ta sama ta fannin tattalin arziki da kuma zaman lafiya, kuma dangane da wannan ziyarar tashi ne Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Dr Abarshi Magalma ga kuma yanda hirers ta kasance.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.