Faransa-Nijar-Chadi

Hollande ya kammala Ziyara a yammacin Afrika

Shugaban Faransa François Hollande da Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno.
Shugaban Faransa François Hollande da Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno. ALAIN JOCARD / AFP

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, a yau Assabar ya kammala ziyarar kwanaki uku da ya kawo a wasu kasashen yammacin Afrika guda uku, Cote d’Ivoire da Nijar da kuma Chadi. Shugaban ya kai ziyara a wani sabon sansani a birnin N'Djamena, inda Faransa zata girke dakarunta da zasu yi yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Talla

A ziyarar da ya kai a Nijar, shugaban na Faransa ya tallafawa kasar da kudade da suka kai kimanin euro miliyan 75 domin inganta kiwon lafiya da ilmi da ayyukan noma da samar da makamashi da kuma wasu ayyukan da zasu kawo ci gaba ga al’ummar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.