Najeriya

A Najeriya kwanaki 100 cur da sace 'yan matan Chibok

'Yan matan Chibok da Boko Haram ta sace.
'Yan matan Chibok da Boko Haram ta sace.

Yau aka cika kwanaki 100 da sace dalibai mata kusan 300 a garin Chibok da ke jihar Borno ta Tarayyar Najeriya inda har yanzu ba’a ji duriyar akasarinsu ba.

Talla

A ranar talata shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da iyayen daliban da kuma wasu daga cikin daliban da suka tsira inda ya sake jaddada musu cewar gwamnati ta san inda daliban suke sai dai tana kaucewa amfani da karfi ne wajen ceto su dan kada a jikkata su.

Bayan ganawar ta ranar talataa, daya daga cikin shugabannin al’ummar ta garin Chibok zuwa fadar shugaban kasar Mr Tsambido Hosea, ya ce a halin gaskiya suna a cikin bakin ciki, sakamakon yadda aka dauki wannan dogon lokaci ba tare da an ‘yantar da ‘yayansu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.