Najeriya

Ebola: An kwantar da wani Dan Liberia a Asibitin Lagos

Jami'an kiwon lafiya da ke awon jinin cutar Ebola a kasar Saliyo
Jami'an kiwon lafiya da ke awon jinin cutar Ebola a kasar Saliyo REUTERS/Umaru Fofana

An kwantar da wani dan kasar Liberia a wata asibitin Lagos wanda ke fama da rashin lafiya mai kama da cutar Ebola. Kodayake har yanzu hukumomin lafiya a Najeriya ba su tabbatar da cutar ta Ebola ce da ke kisan al’umma.

Talla

Likitoci da ke kula da lafiyar Mutumin mai shekaru 40, sun ce yana fama da amai da gudawa bayan ya shigo Najeriya a ranar Lahadi daga Liberia.

Yanzu haka an dauki samfurin jininsa zuwa kasar Sanegal domin tantance ko Cutar Ebola ce.

Mutumin ya shigo Lagos ne ta Lome daga Manrovia kasar Liberia.

Hukumar lafiya ta duniya tace sama da mutane 900 ne suka kamu da cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afrika. Kuma kimanin mutane 172 ne suka kamu da cutar a kasar Liberia bayan bulluwar cutar a Jamhuriyyar Demokuradiyar Congo zuwa Guinea Conakry.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.