Libya

Gobara na ci a defon mai na birnin Tripoli

Tripoli a kasar Libya
Tripoli a kasar Libya REUTERS/Hani Amara

Har zuwa safiyar yau litinin, wuta ta ci gaba da ruruwa a wani defon man fetur da ke wajen birnin Tripolin kasar Libya a daidai lokacin da bangarorin mayaka ke ci gaba da gwabza kazamin artabu domin kama filin sauka da tashin jiragen saman birnin.  

Talla

Tun a ranar lahadin da ta wuce ne wani makami ya fada akan defon mai dauke da sama da lita milyan shidda na mai, a wani wuri mai tazarar kilomita 10 tsakanin Tripoli da kuma filin saukar jiragen saman birnin, lamarin da kwararri ke fargabar cewa zai iya zama babban bala’I matukar dai ba a dauki matakan gaggawa na shawo kansa ba.

Mai magana da yawun kamfanin man fetur na kasar ya ce jami’an kashe gobara sun yi iya kokarinsu domin murkushe gobarar amma lamarin ya buwaya, kuma tuni suka bar wurin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.