Guinea Conakry

Taron hana yaduwar Ebola a Yammacin Afirka

Ebola ta yi kisa a Liberia
Ebola ta yi kisa a Liberia REUTERS/Samaritan's Purse/Handout via Reuters

Kasashen yammacin Afirka na gudanar da taro na musamman kan dubarun hana yaduwar cutar Ebola a birnin Conakry na kasar Guinee daya daga cikin kasashe uku da cutar ta zama annoba.

Talla

Wakilai daga kasashen Guinee, Liberia, Sierra Leone, Cote D’Ivoire da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ne ke halartar taron a wannan juma’a, a daidai lokacin da cutar ta kashe mutanen da yawansu ya haura 700 a yammacin Afirka kawai.

Kafin ranar 27 ga watan yulin da ya gabata, cutar ta kashe mutane 729, (339 a Guinée, 233 a Sierra Leone, 156 a Liberia, sai kuma daya a Nigeria), kamar dai yadda alkalumman Hukumar Lafiya ta duniya suka tabbatar.

Tuni dai Hukumar ta ware Dala milyan 100 domin taimaka wa wadannan kasashe a kokarin da ake na hana yaduwar cutar a cewar Margaret Chan babbar jami’ar hukumar da ke gabatar da jawabi ga mahalarta taron na Conakry, yayin da ta bukaci gwamnatocin kasashen da su matsa kaimi domin samun nasarar murkushe cutar baki daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI