Shugaban Jamhuriyar Nijar Issifou Mahamadou wanda ke gabatar da jawabin cikar kasar shekaru 54 da samun 'yanci a ranar 3 ga watan Agustan 2014, ya ce gwamnatinsa za ta kaddamar da shirin rage haihuwar jama'a sakamakon yadda karuwar jama'a ke tauye ci gaban kasar.Mahaman Salisu Hamisu ya zanta masani dokokin kasar ta Nijar Maitre Lirwana Abdourahman domin jin ko akwai wani hurumi na doka da shugaban zai dogara da shi domin tilasta wa al'ummar kasar kayyade iyali.