Ebola

Dokar ta baci a Saliyo da Liberia da Najeriya

Ana aikin binne wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo
Ana aikin binne wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo REUTERS/WHO/Tarik Jasarevic

Kasashen Liberia da Saliyo da Najeriya sun kafa dokar ta baci domin dakile bazuwar cutar Ebola da ke kisan Jama’a. Gwamnatin Najeriya ta ce tana iya bakin kokarinta wajen dakile yaduwar cutar bayan ta  hallaka mutane biyu a birnin Lagos.

Talla

‘Yan Majalisa a kasashen Liberia da kasar Saliyo zasu yi zama na musamman domin amincewa da dokar ta bacin da shugabanin kasashen suka ayyana don yaki da cutar ebola da yanzu haka ta kashe mutane 932.

Gwamnatin kasar Saliyo ta tura dakarun soji asibitoci da kan iyaka don samar da tsaro a yakin da ake da cutar.

Tuni gwamnatin Jihar Lagos ta nemi malaman addini da su dakatar da tarukan da suka shafi jama’a da yawa don hana yaduwar cutar, yayin da al’ummar birnin ke ci gaba da nuna fargaba ganin yadda cutar ke halalka jama’a a wasu kasashe.

Cutar Ebola ta bulla a Najeriya bayan wani mutumin Liberia ya shigo da cutar a birnin Lagos, birni mafi yawan Jama’a a Najeriya.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace zata gudanar da wani taro a makon gobe kan yadda za’a samo hanyar amfani da wasu gwaje gwaje don dakile yaduwar ebola a Afrika ta Yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.