WHO ta kaddamar da dokar ta baci akan Ebola
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta kaddamar da dokar ta baci akan cutar Ebola da ke kisan Jama’a a yammacin Afrika tare da neman tallafi daga kasashen duniya domin magance bazuwar cutar musamman a kasashen da Ebola ta zama annoba.
Wannan matakin na WHO na zuwa ne bayan Jami’an hukumar sun kammala wani taron gaggawa a Geneva game da Ebola. Hakan kuma na nufin Hukumar zata haramta wa mutane shiga wasu kasashe a yammacin Afrika akan matakan dakile yaduwar cutar da ta hallaka mutane kusan 1,000 a kasashe Uku.
Tuni Kungiyar Likitoci ta Doctors Without Borders ta bayyana cewa cutar Ebola ta zama annoba a yammacin Afrika kuma tana iya bazuwa zuwa wasu kasashe.
Cutar Ebola ta kashe mutane da dama a Guinea da Liberia da Saliyo, yayin da kuma ta kashe mutane biyu a Najeriya. Tuni wadannan kasashen suka kafa dokar ta baci domin yaki da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu