WHO

Ebola: Mutane 56 sun mutu cikin kwana biyu

likitoi suna tantance Fasinjan Jirgin sama  à Abidjan
likitoi suna tantance Fasinjan Jirgin sama à Abidjan REUTERS/Luc Gnago

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana matukar damuwarta a game da yadda cutar Ebola ke ci gaba da tsananta a kasashen yammacin Afirka. Hukumar ta ce a cikin kwanaki biyu da suka gabata kawai, cutar ta kashe mutane 56 a wadannan kasashe.

Talla

Hukumar ta lafiya ta bayyana cewa a halin yanzu mutane 1069 ne suka rasa rayukansu yayin da aka samu karin wasu mutanen 128 da ke ci gaba da jinya sakamakon kamuwa da cutar.

Mutane 32 daga cikin wadanda suka mutu cikin kwanaki biyu ‘yan kasar Liberia ne sai kuma 19 a kasar Saliyo.

Guinea Conakry, wato kasa ta farko da cutar ta soma bulla a yammacin Afirka, ta ce tana a cikin bukatar samun taimakon kasashen duniya domin tunkatar wannan cuta da ta kashe daruruwan mutane a kasar.

Albert Damantang Camara, s kakakin gwamnatin kasar ta Guinea yace Kasashen duniya na dari-dari wajen kawo wa Guinea dauki, yayin da sauran suka takaita zirga-zirgarsu, wannan ya yi matukar shafar kokarin da ake yi domin tunkarar wannan matsala a kasar Guinea da kuma sauran kasashe na wannan yanki.

Duk da cewa ba wasu rahotanni da ke tabbatar da cewa cutar ta bulla a yankin gabashin Afirka, amma Hukumar lafiya ta yi gargadin cewa, kasantuwar kasar Kenya cibiya da kasashen yankin ke amfani da ita ta fannin zirga-zirga da dai sauransu, akwai bukatar daukar matakai a cewar Uwargida Custodia Man, shugabar ofishin hukumar lafiya a Nairobi.

Yanzu haka ana jiran isowar wata allurar maganin wannan cuta ta Ebola zuwa yammacin Afirka daga kasar Canada, yayin da ita ma Amurka za ta turo wani a cikin sa’o’I 48 ma su zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.