Ebola

Cutar Ebola annoba ce a Afrika-WHO

Jami'an lafiya da ke kula da cutar Ebola a Guinéa
Jami'an lafiya da ke kula da cutar Ebola a Guinéa T. Jasarevic/OMS

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace girman Cutar Ebola da ke bazuwa a yammacin Afrika ya zarce tunanin mutane tare da kiran daukar matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar da ta kashe mutane 1,069.

Talla

Kasar Amurka ta bayar da umurnin a kwashe Jami’an diflomasiyarta daga Saliyo, daya daga cikin kasashen da Cutar Ebola ta yi kisa da yawa.

A cikin wata sanarwa, hukumar lafiya ta duniya WHO tace tana nazarin yadda za’a magance yaduwar cutar a kasashen duniya.

Najeriya ita ce kasa da hudu da aka samu bullar cutar Ebola bayan shigowar wani dan kasar Liberia a Lagos, kuma yanzu mutane hudu aka tabbatar da mutuwarsu.

Cutar Ebola na iya sa kamfanonin Mai ficewa daga Najeriya da ke aiki a Lagos, kamar yadda kamfanin Moody da ke auna karfin tattalin arzikin kasashen duniya ya yi gargadi.

Sakamakon barazanar da cutar Ebola ke yi a yankin yammacin Africa, shugaban Amurka Barack Obama ya tattauna da wasu shugabannin kasashen yankin da cutar ke yin kisa game da batun yadda za’a shawo kanta.

Mr Obama ya yi Magana da shugabar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf da Ernest Bai Koroma na Saliyo, don duba yadda za a shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.