Isa ga babban shafi
Najeriya

Likitoci sun yi zanga-zanga a Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
1 min

Likitocin sun gudanar da wannan zanga-zangar ne domin nuna bacin ransu a game da wannan mataki, kwana daya bayan da gwamnatin tarayyar ta sanar cewa ta kori wasu likitoci dubu 15 daga aiki ba tare da an gabatar da hujjojin yin hakan ba a cewarsu.

Talla

Sanarwa da sakataren dindindin na ma’aikatar kiwon lafiyar Najeriya ya sanya wa hannu a ranar 13 ga wannan wata nan agusta, ta bukaci manyan jami’an cibiyoyin kiwon lafiya da kuma asibitocin gwamnatin tarayya da su gaggauta sallamar dukkanin likitocin da wannan umurni ya shafa.

Wata majiya dai ta bayyana cewa tuni gwamnati ta yi shirya biyan likitocin albashinsu wata daya domin shafe masu hawaye.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.