Najeriya

Amnesty ta ce bankin duniya da gwamnatin Lagos sun tauye hakki

Birnin Lagos
Birnin Lagos DR

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta zargin Bankin Duniya da kuma gwamnatin jihar Lagos da kauce wa ka’ida wajen biyan diyya ga dubban mutanen da aka kora daga muhallansu da ke unguwar Badia da ke birnin Lagos kimanin shekaru biyu da suka gabata.

Talla

Kungiyar ta zargi Bankin na duniya da kawar da kai dangane da mutunta dokokin da suka shafi kare hakkokin bil’adama, inda ya marawa gwamnatin ta jihar Lagos wajen tauye jama’ar hakkokinsu.

Kimanin shekaru biyu da suka gabata ne gwamnatin ta jihar Lagos ta kaddamar da wani shirin kawar da wasu dubban gidaje a cikin birnin mai cinkoson jama’a, kuma unguwar Badia East na a matsayin wadda wannan shiri ya fi shafa inda dubban mutane suka rasa muhallansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI