Ethiopia

Kasar Habasha ce ta fi ko wace kasa yawan yan gudun Hijira a duniya

Reuters

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce a halin yanzu kasar Habasha ce, kasar da ta fi kowace kasa karbar ‘yan gudun hijira a duniya, musamman idan aka yi la’akari da yadda wasu dubban yan gudun hijira daga kasar Sudan ta kudu suka tallaka zuwa cikin kasar. Bayan wadanda ke cikin kasar a baya da suka tserewa yake yaken da ake tabkawa a kasar Somaliya. Hukumar yan gudun Hijirar ta ce, kawo yanzu ‘yan gudun hijira dubu 629 da 718 ne, suka ke zaune a kasar, sabanin kasar Kenya mai yawan yan gudun hijira dubu 575 da 334. Wace da farko it ace kan gaba