Libya

An rufe gidajen Telebijin biyu a Libya

Mayakan zintan na Libya
Mayakan zintan na Libya REUTERS/Hani Amara

Hukumomin Kasar Libya sun sanar da rufe wasu gidajen talabijin biyu da suka ce ‘Yan Tawaye sun kwace a birnin Tripoli. Wani jami’in kasar ya bayyana kafofin a matsayin tashar Libya al Wataniya da ke hannun gwamnatin riko da Libya al Ramia da ke karkashin Majalisar kasa.

Talla

Mahukuntan kasar Libya sun rufe tashoshin biyu ne saboda sun bayyana goyan bayan ga ‘Yan Tawayen da ke yaki da gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI