Sudan

Kabilun Darfur sun yi gumurzu

Wata Mata da aka kona muhallinta a yankin Darfur
Wata Mata da aka kona muhallinta a yankin Darfur REUTERS/Albert Gonzalez Farran/ys

Wani kazamin fadan kabilanci da ya kaure tsakanin wasu kabilun Larabawa biyu da ke gaba da juna a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, kamar yadda shaidu daga bangarorin biyu suka tabbatar.

Talla

A kalla mutane 30 ne daga kabilar Rzigat aka kashe a cikin fadan kabilanci da ya hada su da abokan gabarsu yan kabilar Ma’aliya d ake yankin Oum Rakuba sakamakon kokarin mallakar filaye kamar yadda shaidu daga kabilar ta Rzigat suka tabbatarwa Kamfanin Dillacin labaru na Faransa.

Wani shaida daga kabilar ta Ma’aliya kuma ya yace mutanensu 40 ne aka kashe a fadan, sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wadannan sakamako da bangarorin biyu suka bayar

Rikicin da ake fama da shi a Darfur yankin da ke da taswirarsa ke da matukar fadi fiye da kasar Faransa, ya barke ne tun cikin 2003 tsakanin dakarun sa-kai da ke goyon bayan gwamnatin Khartoum, da ‘yan tawayen da ke bukatar kawo karshen mamaye tattalin arzikin yankinsu ta hanyar yin raba daidai tsakaninsu da gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI