Najeriya

Sheriff da Ihejirika ke daukar nauyin Boko Haram, inji Davis

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP

Wani Batturen kasar Australia Stephen Davis da ke jagorantar tattaunawa da Mayakan Boko Haram domin kubutar da ‘Yan matan garin Chibok da aka sace a Jihar Borno, ya shaidawa wata Kafar Telebijin cewa Tsohon Gwamnan Jihar Borno Senata Ali Modu Sheriff da tsohon babban hafsan Sojin kasar Janar Azuburike Ihejirika a matsayin wadanda ke daukar nauyin Mayakan Boko Haram.

Talla

A wata hira ta musamman, Davis ya shaidawa kafar Telebijin ta Arise News cewa mutanen biyu suna da hannu ga ayyukan Boko Haram a Najeriya tare da kira ga gwamnatin Najeriya ta kaddamar da bincike akai.

A cikin hirar, Mr Davis yace wasu ‘Yan siyasa a Najeriya suna da hannu dumu dumu a rikicin na Boko Haram.

Amma wasu Jaridun Najeriya sun ruwaito tsohon babban hafsan sojin kasar yana mayar da martani. Jaridar Vanguard da ake bugawa a kudancin kasar ta ruwaito Janar din yana karyata zargin tare da caccakar tsohon Ministan Abuja Nasir El Rufa’I wanda ya fara saka labarin a shafin shi na Facebook game da tattaunawar Mr Davis da kafar Telebijin ta Arise News.

Amma a cikin tattaunawar baturen na Australia ya bayyana yadda ya ke tattaunawa da Boko Haram tare da kira ga gwamnatin Najeriya ta cafke Modu Sheriff wanda ya ce da dadewa ne ya ke daukar nauyin ayyukan Boko Haram.

Mr Davis ya ambaci tsohon shugaban rudunar Sojin Najeriya wanda ya yi ritaya a watan Janairu a matsayin daya daga cikin masu hannu a rikicin Boko Haram.

Baturen ya bayyana irin tallafin da Mayakan na boko Haram ke samu daga ‘Yan siyasa a Najeriya suka hada da tallafin Kudi da motoci kirar Hilux.

A cikin tattaunawar, Davis yace ya yi aiki da shugabannin Najeriya da suka gabata, Musulmi da Kirista amma kuma yanzu yana mamakin yadda abubuwa ke tafiya.

A cewarsa babban kalubalen da ya ke tunanin Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke yin fargaba akai shi ne samun baraka idan har ya fara cafke ‘Yan siyasa akan Boko Haram.

“Idan ya fara cafke manyan ‘Yan siyasa da ke son fafatawa da shi a zabe mai zuwa, manyan kasashen duniya Faransa da Birtaniya da Amurka zasu fara zarginsa akan yana karya ‘Yan adawa don ya ci zabe".

Davis yace akwai wadanda ke da hannu wajen sace ‘Yan matan Chibok amma akwai dubarun da ya ke bi wajen tattanawar ganin an kubutar da ‘Yan Matan.

Amma Janar Ihejirike ya shaidawa Jaridar Thisday cewa wannan wani salon ne na karkatar da hankalin duniya da ke kokarin ganin an kawo karshen rikicin Boko Haram a Najeriya bayan ya yi watsi da zargin.

A ranar Lahadi ne Shugaban Boko Haram ya yi ikirarin kafa sabuwar daula bayan Mayakansa sun karbe ikon garuruwan Gwoza da Gamburu-Ngala a jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI