Lesotho

Kungiyar SADC na shiga tsakani a rikicin Lesotho

Firaministan Lesotho, Thomas Thabane
Firaministan Lesotho, Thomas Thabane AFP PHOTO / GCIS / ELMOND JIYANE

Taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar ci gaban yankin kudancin Afirka wato SADC ya amince da aikewa da wata tawaga zuwa kasar Lesotho kwanaki biyu bayan da Firaminstan kasar ya ce an yi masa juyin mulki.  

Talla

A sanarwar da aka fitar bayan kammala wannan taro, ta bayyana cewa babbar manufar aikewa da wannan tawaga ita ce shiga tsakanin bangarorin da ke hannu a wannan rikici.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Firaministan Tom Thabane ke cewa zai koma kasar daga Afrika ta Kudu inda yake gudun hijira.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI