Isa ga babban shafi
Nijar

Hama Amadou ya zargi Shugaba Issifou da yunkurin kashe shi

Mahamoud Issoufou da kuma Hama Hamadou lokacin yakin neman zaben shekara ta 2011.
Mahamoud Issoufou da kuma Hama Hamadou lokacin yakin neman zaben shekara ta 2011. AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA

Shugaban Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar Hama Amadou wanda ake zargi da fataucin jarirai, yanzu haka yana birnin Paris na kasar Faransa, kuma a zantawarsa da mujallar Jen Afrique, ya zargi shugaba Isifu Mahamadu da yunkurin kashe shi ta hanyar sanya masa guba.

Talla

Hama Amadou daya daga cikin masu adawa da shugaba Isifu Mahamamdu, ya gudu ya bar kasar ne a ranar 27 ga watan jiya, a daidai lokacin kwamitin gudanarwar majalisar dokokin kasar ke zama domin mika shi a hannun kotu da ke zarginsa da sayo jarirai domin mayar da su ‘yayansa.

To a zantawarsa da mujallar ta jeune Afrique, Hama Amadou ya bayyana cewa dalilin kirkiro wannan batu shi ne kama shi domin tsare shi a gidan yari, kafin daga bisani a sanya masa guba domin kashe shi.

Da aka tambaye shi ko watakila shugaba Isifu Mahamadu na da masaniya a game da wannan yunkuri na kashe shi, sai ya ce ko shakka babu shugaban na da masaniya, kuma tuni aka shigo da wannan gubar daga kasar Libya, wadda za a sanya masa a abinci lokacin da yake tsare, kuma irin wannan gubar a cewarsa ba za ta yi wa mutum illa ba sai bayan watanni da dama.

Har ila yau shugaban majalisar dokokin na jamhuriyar Nijar ya musanta cewa shi ko matarsa na da hannu a fataucin jarirai, inda ce kowa ya tabbatar da cewa matarsa ta dauki ciki na halas har ma ta haife shi kafin wannan batu na cikin jarirai ya kunno kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.