Saliyo

Ebola: Ma’aikatan Asibiti sun shiga yajin aiki a Saliyo

Likitoci suna kula da masu cutar Ebola a Libéria.
Likitoci suna kula da masu cutar Ebola a Libéria. UNFPA Libéria

Ma’aikata a wata asibitin kula da wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo sun shiga yajin aiki saboda kin biyansu kudadensu na albashi duk da sun sadaukar da rayuwarsu ga aikin kawar da Cutar Ebola da ke kisan mutane da dama a kasar.

Talla

Gwamnarin Saliyo ta dauki Ma’aikatan ne na wuccin gadi domin taimakawa ma’aikatan jinya da likitoci a Asibitin Kenema da ake kula da lafiyar majinyantan Ebola.

Wasu daga cikin Ma’aikatan sun yi koken cewa tun lokacin da suka fara aiki babu sisin kwabo da aka biya su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.