Najeriya

Afruka ta kudu ta sake kwace wasu kudin sayen Makamai daga Najeriya

A tarayyar Najeriya bayan da ake ci gaba da takaddama akan kudin sayen Makamai Dala Miliyan 9 da doriya, da kasar Afruka ta kudu ta kwace daga wasu ‘yan Najeriya da dan kasar isra’ila a wani Jirgi mallakar shugaban kungiyar Kiristocin kasar da aka nufi sayen Makamai da su ba bisa ka’ida ba, yanzu haka kasar ta Afruka ta kudu ta sake kwace wasu kudin da suma aka yi niyyar sayen Makamai da su

RFI Hausa
Talla

Yanzu haka dai ana ci gaba da yi wa hukumomin kasar matsin lamba dangane da bayanai da ke cewa kasar ta Afirka ta kudu masu cewar kasra ta sake kama wasu makuddan kudi da yawansu ya kai kusan Dala milyan 6 wadanda ake shirin sayo makamai da su.

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da neman hukumomin kasar sun yi wa al’umma karin haske dangane da wadancan mutane 3 da aka kama dauke da wadancan makudan kudade da manufar sayo wasu makamai.

Barrister Solmon Dalung, Babban lauya kuma mai fafutukar kare kare hakkin bil’adama a Najeriyar daga yankin Arewacin kasar, ya ce dole ne gwamnati ta yi wa al’ummar kasar bayani kan wannan a’lamari.

Batun sayen Makaman dai na ci gaba da tada Jijiyoyin Wuya a tsakanin ‘yan kasar musamman daga yankin Arewacin kasar masu yiwa shugaban kasar kallon mai yin balulluba ga shirin sayen makaman da kungiyar Kiristocin kasar ke yi da wata manufa ta kara zafafa tashin hankali a kasar mai fama da hare-haren ‘yan Boko Haram.

A baya dai akwai wani jagoran wata kungiya a yankin Niger Delta Dokubo Asari da ya taba kiran taron manema labarai yana bayyanawa karara cewar idan shugaba Jonathan bai zarce ba, to babu sauran zaman lafiya a kasar, harma ya lissafa muhimman mutane daga yankin Arewacin kasar da suke da niyyar hallakawa ciki kuwa hadda tsohon shugaban kasar Janar Muhammadu Buhari.

Harin baya-bayan nan da aka kaiwa janar Buhari da Shaihin Malami Shaikh Attahiru Usman Bauchi a Kaduna ya sa mutane tunanin wata kila alwashin da su Dokubo Asari suka yi ne suke shirin kammalawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI