Kenya

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya zai bayyana a Kotun ICC yau Laraba

Rais wa Kenya, Uhuru Kenyatta akizungumza wakati wa sherehe za madaraka day juma hili
Rais wa Kenya, Uhuru Kenyatta akizungumza wakati wa sherehe za madaraka day juma hili Kenyagvt

A yau laraba ne shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta zai gurfana a gaban kotun hukunta masu manyan laifufuka ta Duniya da ke birnin Haugen na kasar Holland

Talla

Wannan dai shi ne karo na farko da wani shugaban kasa da ke kan karagar mulki ya gabatar da kansa a gaban wannan kotu.

Shugaba Uhuru wanda ya isa kasar ta Holland a jiya talata, yana daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu wajen tayar da rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 1, bayan kammala zaben shugabancin kasar ta Kenya a shekara ta 2007, kuma tuni ya danka ragamar shugabancin kasar a hannun mataimakinsa William Ruto kafin ya gabatar da kansa a gaban kotun.

Masu sharhi kan lamurran yau da kullum dai na ganin gurfanar shugaban a matsayin wani shiryayyen abu na kokarin wanke shi daga laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Al’ummar kasar Kenya dai na matukar son shugaba Uhuru kenyatta musamman lura da yanda ya dauko matakan daidaita kasar daga matsalolin da ta yi fama da su a baya, na karayar tattalin arziki, da kuma samar da zaman lafiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.