Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai koma gida daga ICC

nairobiwire.com

Yanzu haka shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata na kan hanyarsa ta komawa birnin Nairobi Kenya yau da safe bayan da ya halarci zaman kotun kasa-da-kasa da ke zarginsa da hannu wajen tarzomar da ta barke tsakanin shekara ta 2007-2008

Talla

A wannan lokacin dai an bayyana kisan akalla mutane Dubu da 200, a wani abinda ake zargin shi Uhuru Kenyatta da Hannu ga aikatawa ta hanyar tunzura mutane tashin hankali da a lokacin bai yiwa hukumomin kasa-da-kasa dadi ba.

Uhuru Kenyata wanda ya damka iko ga mataimakinsa, kafin ya tafi Hague domin sauraron zaman kotun, ya kasance shugaban kasa na farko daya gurfana gaban kotun tare da lauyoyin sa.

 

Masu lura da al'amurra dai na yiwa Kotun kallon Karyar farautar kasashen yammacin Duniya kan shugabanni a yankin Nahiyar Afruka, lura da cewar ba'a taba samun shugaba ko daya daga Turai da Kotun ta gurfanar ba, duk da cewa ko ma a can akan samu shugabanni masu mulkin kama-karya.

Akawai ma masu hangen cewar ya kamata mazaunin Kotun ya kasance a Afruka a maimakon wani yanki na Nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.