EQUATORIAL GUINEE

Amaruka ta soke tuhumar da take yiwa Theodoro Obiang

Theodoro Obiang,Dan Shugaban kasar Equatorial Guinee.
Theodoro Obiang,Dan Shugaban kasar Equatorial Guinee. Photo: AFP/Abdelhak Senna

Theodoro Obiang dan Shugaban kasar Equatorial Guinee ya amince bayan cimma wata yarjejeniya tsakani sa da gwamnatin Amaruka na yafe kusan dala kudin amaruka milliyan 30. Ana dai tuhumar dan tsohon Shugaban kasar da karkata wasu kudade kasar . 

Talla

Gwamantin Amaruka ta tilasta masa saida wasu daga cikin kadarorin sa da suka hada da wani kasaitacen gida a California na kasar Amaruka da wasu kayakin tarihi na kusan milliyan 20 na dalla .

Yanzu haka banda Amaruka ,Faransa na daga cikin kasashe dake gudanar da bincike kan wasu Shugabanin kasashen Afrika da suka hada da Congo Brazaville,Equatorial Guinee, da tsohon Shugaban Gabon Marigayi Omar Bongo na malakar haramtaciyyar Dukiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.