Najeriya

Bicinke kan wani harin sojoji a Najeriya

Sojin Najeriya
Sojin Najeriya

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama a Najeriya sun bukaci gwamnatin kasar ta kaddamar da binciken gaggawa kan yadda sojoji suka bude wuta a unguwar marasa karfi dake Abuja. Rahotanni sun ce wani Kaftin na soji ne ya jagoranci kai harin inda sojojin su kayi ta harbi kan mai uwa da wabi da kuma kama wasu matasa da dama.

Talla

Wasu daga cikin wadanda suka samu harbin bindigan sun ce basu san dalilin kai harin da sojojin suka yi ba. Idan ba'a manta ba sojojin da jami'an hukumar tsaron farin kaya sun kai irin wannan harin wani gini inda suka kashe matasa da dama a Abuja matakin da hukumar kare hakkin Bil Adama ta bayyana shi a matsayin haramtacce kuma ta bukaci biyan diyya. Ko a watan jiya sai da kungiyar Amnesty International ta sake zargin sojojin Najeriya da kashe fararen hular da ba suji ba su gani ba zargin da sojin suka musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.