'Yan matan Chibok sun cika wata 6 a hannun 'yan Boko Haram

Wasu masu kokarin ganin an ceto 'yan Matan Chibok daga hannun 'yan Boko Haram
Wasu masu kokarin ganin an ceto 'yan Matan Chibok daga hannun 'yan Boko Haram REUTERS/Afolabi Sotunde

A Najeriya, yau watanni 6 kenan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da wasu ‘yan mata sama da 200 a makarantar Sakandaren garin Chibok da ke cikin jihar Borno.To sai dai watanni shida da faruwar wannan lamari, har yanzu ba wata alama da ke tabbatar da cewa hukumomin tsaro na gaf da ‘yantar da wadannan ‘yan mata.Wannan ya sa masu zanga zangar neman ganin an sako wadannan ‘yan matan, ke ci gaba da matse kaimi, inda ake fatan yau Talata zasu mika wa shugaban kasar Goodluck Jonatahan bukatar ganin an ceto ‘yan matan.