Afrika ta Kudu

Batun rabon gadon tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu marigayi Nelson Mandela da sake inji tsohuwar matarsa Winnie

Nelson Mandela est libéré après 27 ans d'incarcération. Ici avec son épouse Winnie, le 1er février 1990.
Nelson Mandela est libéré après 27 ans d'incarcération. Ici avec son épouse Winnie, le 1er février 1990. Allan Tannenbaum

Winnie Mandela mai shekaru 78, ta bukaci kotu ta mallaka mata gidan marigayi Nelson Mandela dake Qunu kauyensa na haihuwa, domin acewar ta ita ta sayi gidan a yayin da Mandela ke tsare a gidan yari  

Talla

Gidan da aka binne gawar Mandela na daga cikin kadarorin da aka dankawa amaryarsa Graca Machel wadda ya mutu suna tare

A karar da tsohuwar matarsa Winnie ta shigar tace gidan halaliyarta ne, inda ta nemi kotu data cire shi daga jerin kadarorin gado da Mandela ya barwa sauran iyalansa

Winnie Madikizela Mandela dai ta auri Nelson Mandela a 1958,kuma tsakaninsu akwai yara mata biyu, ta kuma taka mahinmiyar rawa a gwagwarmayar Nelson Mandela wajen kawar da tsarin wariyar launin fata a kasar ta Africa ta kudu

Aure tsakanin Mandela da Winnie ya mutu ne, a 1996 bayan Mandela ya zama shugaban kasa.

Sai dai duk da haka Winnie ta kasance da tsohon mijin nata a lokacin da yake jinya har mutuwarsa

Game da batun gado babu sunan Winnie acikin jerin sunayen mutanen da Mandela ya barwa kudi da kadarori da darajarsu ta kai sama da dala miliyan 4

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.