Tanzania-Burundi

Sama da yan gudun hijirar kasar Burundi dubu 200 ne Tanzaniya zata baiwa takardun zama yan kasarta

Burundi-Dandazon ayarin yan gudun hijirar Burundi dake tsrewa kisan kiyashin kasar zuwa Kongo [nid:500476298]
Burundi-Dandazon ayarin yan gudun hijirar Burundi dake tsrewa kisan kiyashin kasar zuwa Kongo [nid:500476298]

Kasar Tanzania za ta bai wa ‘yan gudun hijirar kasar Burundi sama da dubu 200 takardar shaidar zama dan kasar, matakin da tuni MDD ta jinjinawa.  

Talla

Sanarwar da hukumomin kasar ta Tanzania suka fitar a jiya talata, ta bayyana cewa wadanda za a bai wa takardar shaidar zaman dan kasar, dukkaninsu ‘yan gudun hijira ne da ke zauna a kasar tun a shekarar 1972.

Ministan cikin gidan Tanzania Mathias Chikawe ya ce a jimilce akwai ‘yan kasar ta Burundi su akalla dubu 162 da suka gabatarwa hukumomi bukatunsu ta son samun takardar shaidar zama dan kasar.

A marecen jiya ne dai, shugaban kasar Jakaya Kikwete ya jagoranci bikin bayar da takardun shaidar zama dan kasar ga kashin farko, na ‘yan kasar ta Burundi a birnin Dares Salam.

Tanzania dai, na a matsayin daya daga cikin kasashen Afirka da suka fi bai wa ‘yan gudun hijira mafaka, kuma da dama daga cikinsu ‘yan kasar ta Burundi ne da suka gujewa yakin basasa da kuma kisan kare dangi da ya faru a cikin shekarun 1990.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.