Cote d'Ivoire

Za'a gurfanar da matar tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo, cewa da Simone Gbagbo a gaban Kotu

Matar tsohon shugaban Cote d’Ivoire Laurent Bagbo wato Simone Bagbo wadda ita ma ake zargi da hannu wajen tayar da rikicin da ya barke bayan kammala zaben shugabancin kasar na 2010, za ta gurfana gaban alkali karo na farko a ranar 22 ga wannan wata na okotba.

Talla

Ko baya ga Simone Bagbo akwai wasu tsoffin jami’an gwamnatin kasar su akalla 90 da za a soma yi wa shari’a a ranar, kamar dai yadda daya daga cikin lauyoyinsu Herve Guamene ya bayyana a birnin Abidjan.

Tun kafin wannan lokaci dai, ake ta ja’injar inda za a gurfanar da matsar tsohon shugaban kasar tsakanin kotunan kasar da kotun duniya, inda aka gurfanar da mijinta

Simone Bagbo dai na daya daga cikin wadanda ake zargi da haddasa fitinar zaben da ta yi sanadiyar hasarar dubban rayukan al’ummar kasar ta Cote D’Ivoire a 2010
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.