Guinea Conakry

karanci jam'ian kiwon lafiya a Guinee

Shugaban kasar Guinée Alpha Condé.
Shugaban kasar Guinée Alpha Condé. presidentalphaconde.com

Hukumomi a kasar Guinee Conakry daya daga cikin kasashen da ke fama da cutar ta Ebola, sun bukaci illahirin jami’an kiwon lafiyar da suka yi ritaya da su koma baki aiki domin taimakawa a yaki wannan annoba.

Talla

Shugaban kasar Alpha Conde ne ya yi wannan kira zuwa tsofaffin jami’an kiwon lafiyar a dai dai lokacin da cutar ke neman shan karfin jami’an lafiyar kasar.
Yayi da kasashen Duniya suka sanar da daukar dukkanin matakan da suka wajaba domin tunkarar wannan annoba da kawo yanzu ta kashe sama da mutane dubu 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.