Cote d'Ivoire

Mahaifiyar Laurent Bagbo ta rasu

Mahaifiyar tsohon Shugaban Cote D'ivoire Laurent Bagbo
Mahaifiyar tsohon Shugaban Cote D'ivoire Laurent Bagbo

A kasar Cote d’Ivoire mahaifiyar tsohon shugaban kasar wanda yanzu haka ke tsare a hannun kotun duniya wato Laurent Bagbo ta rasu a jiya laraba tana da shekaru 90 a duniya.

Talla

A ranar lahadin da ta gabata ne mahaifiyar tsohon shugaban mai suna Marguerite Gado ta isa birnin Abidjan daga kasar Ghana inda take gudun hijra,
Sai dai tuni magoya bayan tsohon shugaban suka soma zargin hukumomin kasar da nuna halin ko in-kula, ta la’akari da cewa wannan tsohuwa ta yi wannan tafiya ne a cikin motar iyalanta a maimakon motar jami’an kiwon lafiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.