Najeriya

Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakani Boko Haram da Gwamnatin Najeriya

Abubakar Shekau Shugaban Kungiyar Boko Haram.
Abubakar Shekau Shugaban Kungiyar Boko Haram. Fuente: YouTube

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Boko Haram sakamakon ganawar da bangarorin biyu suka yi. Ambassada Hassan Tukur Sakataren Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sanar da haka a Saudi Arabiya bayan tattaunawar da suka yi tsakanin bangarorin biyu.

Talla

Daya daga cikin manyan jami’ai a fadar shugaban kasar Goodluck Jonathan mai suna Hasan Tukur, ya tabbatar da kulla wannan yarjejeniya, kuma a cewar sa an cimma wannan matsaya ne sakamakon tattaunawa karo biyu da aka yi tsakanin wakilan gwamnati da na kungiyar a gaban idon shugaban kasar Chadi Idris Deby.
Tukkur ya ci gaba da cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun amince su saki ‘yan matan sakandaren Chibok 219 da suka kama a tsakiyar watan afrilun da ya gabata.
To sai dai lura da irin sanarwowin da suka saba fitowa daga fadar shugaban kasar da bangaren ma’aikatar tsaro, wannan ya sa manazarta na nuna shakku a game da ikirirarin na yau. Yayin da wasu ke ganin cewa a wannan lokaci da aka buga kugen siyasa, shugaba Jonathan zai yi alfahari da bai wa ‘yan kasar irin wannan labari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.