Najeriya

An kawo karshen cutar Ebola a Najeriya

Jami'an yaki da cutar Ebola
Jami'an yaki da cutar Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce daga yau litinin an shawo kan cutar Ebola a Najeriya, daya daga cikin kasashen da cutar ta bulla a Yammacin Afirka.

Talla

Manzon musamman na hukumar ta lafiya a Najeirya Rui Gama, ya ce an share tsawon kwanaki 42 ba tare da an samu karin wani mutum da ya kamu da cutar ba.

A ranar juma’ar a ta gabata ne hukumar ta lafiya ta sanar da irin wannan labari a game da kasar Senegal, lamarin da ke kara nuni da cewa ana samun ci gaba a kokarin da ake na hana yaduwar cutar a cikin kasashen na yammacin Afirka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.