EQUATORIAL GUINEE

Shugaban Equatorial Guinea yayi afuwa ga 'yan siyasar da suka fice daga kasar

Shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema
Shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Reuters/James Akena

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema, ya sanar da yin afuwa ga dukkanin masu adawa da shi amma suke gudun hijira a kasashen ketare. Kudurin dokar da shugaba Obiang Ingema ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin bai wa illahirin ‘yan siyasar kasar da ke zaune a kasashen ketare damar komawa gida, domin halartar taron mahawara kan lamurran da suka shafi kasar, wanda da za a gudanar a cikin kwanaki goman farkon watan nuwamba mai zuwa.Cikin watan Agusta, shugaba Ingema wanda ya dare kan karagar mulkin kasar tun a shekarar 1979, ya bayyana cewa za a gudanar da babban taro, da zai hada dukkanin ‘yan siyasar kasar, kuma za a bai wa wadanda ke zaune a waje damar halarta.To sai dai bayan da shugaban ya bayyana haka, da dama daga cikin manyan ‘yan siyasar kasar da ke zaune a kasashen waje, sun ce ba za su koma gida ba matukar dai ba a shelanta yin afuwa ga illahirin ‘yan siyasar da ke zaune a waje ba.Shugaban dai ya bayyana cewa wannan taro, zai kasance wata dama domin tattaunawa akan dukkanin batutuwan da suka shafi kasar.