Jam'iyyar ZANU-PF na fuskantar rashin tabbas a Zibabnwe

Mai dakin shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, wato Grace
Mai dakin shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, wato Grace REUTERS/Philimon Bulawayo

Akwai alamun dake nuna cewa babban jam’iyyar dake mulki a kasar Zimbabwe na iya darewa gida biyu, sakamakon jita-jitar dake nuna uwargidan shugaban kasar, Grace Mugabe na neman hawa kujerar mijin nata, Robert Mugabe.An dade ana ganin akwai baraka cikin jamiyyar ta ZANU-PF, gameda wanda zai maye gulbin shugaba Mugabe mai shekaru 90 a duniya.Masu lura da lamurran kasar na ganin akwai rashin jituwa tsakanin uwargida Grace, da kuma mataimakiyar Shugaban kasar Joice Mujuru wadda ake ganin tana iya hawa kujerar, idan har aka sami gibin.Shugaba Mugabe na ci gaba takun saka da kasashen yammacin duniya, sakamakon yadda ya karbe gonakin turawa, ya mallakawa bakaken fata 'yan asalin kasar ta Zimbabwe.