WHO

Za’a samu wadatuwar rigakafin Ebola a 2015

Jami'an kiwon lafiya na yaki da cutar Ebola a liberia
Jami'an kiwon lafiya na yaki da cutar Ebola a liberia REUTERS/James Giahyue

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tace kafin karshen shekara ta 2015 za’a samu wadatuwar dubban rigakafin cutar Ebola mai yin kisa cikin hanzari a kasashen yammacin Afrika. Hukumar tace za’a samar da rigakafin ne kusan Miliyan guda.

Talla

Tun a watan Disemban bana ne za’a fara gwajin rigakafin ga Jami’an kiwon lafiya da suka kamu da cutar.

Amma Hukumar tace babu tabbaci akan ko rigakafin zai kawo karshen cutar.

Hukumar WHO da ke aikin yaki da cutar Ebola a duniya, tace nan da tsakiyar shekara ta 2015 za’a samar da daruruwan rigakafin cutar.

Wannan na zuwa ne a yayin da shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai suka amince da tallafin kudi sama da euro Biliyan guda domin yaki da cutar Ebola a kasashen Afrika.

Mutane kusan 5,000 suka mutu a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo saboda Ebola, kuma masana yanzu sun bayyana fargaba akan barazanar yaduwar Cutar Ebola a kasashen yammacin Afrika.

A cikin makon nan ne aka samu bullar Cutar Ebola a Mali bayan cutar ta bulla a Najeriya.

Kimanin mutane 43 ne ake lura da lafiyarsu a Mali wadanda suka yi mu’amula da wata yarinya ‘Yar shekaru biyu da ta yi sanadin bullar cutar Ebola a cikin kasar daga Guinea.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI