Masar

An kai mummunan hari a Sinai

Sojojin Masar a suna Salla a Sinai
Sojojin Masar a suna Salla a Sinai AFP

Gwamnatin kasar Masar ta kafa dokar ta-baci a sassan yankunan mashigin Sinai bayan mutuwar Sojojin kasar 30 a wani harin kunar bakin wake da Mayaka suka kai a yau Assabar.

Talla

Wannan dai shi ne aka bayyana hari mafi muni da aka kai tun bayan da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi a bara.

Dokar ta bacin ta fara aiki da misalin karfe uku na rana agogon GMT kuma dokar, ta shafi arewaci da tsakiyar Sinai, har zuwa tsawon watanni uku.

Akwai dokar hana fita da aka kafa daga misalin karfe 5 na yamma zuwa 7 na safe.

Gwamnatin Masar kuma tace zata rufe mashigin Rafah zuwa zirin Gaza, hanya guda kacal da ake shiga yankin Falasdinawa ba karkashin ikon Isra’ila ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.