Najeriya

Boko Haram ta sace Yara 30 a Mafa

Wata Dalibar Makarantar Boko a Jihar Borno mai fama da hare haren Boko Haram
Wata Dalibar Makarantar Boko a Jihar Borno mai fama da hare haren Boko Haram Akintunde Akinleye/Reuters

Kimanin yara kanana 30 ne yawancinsu mata ‘yan shekaru 11 Mayakan Boko Haram suka sace a garin Mafa da ke Jihar Borno yankin arewa maso gabacin Najeriya. Hakimin garin Mafa Alhaji Shettima Maina ya tabbatar da sace yaran da suka kunshi maza da mata.

Talla

Wannan kuma na zuwa ne dai dai lokacin da ake kokarin kubutar da ‘Yan mata sama da 200 da Mayakan na Boko Haram suka sace a garin Chibok.

Shettima yace akwai mutane 17 da aka kashe a wani hari da Mayakan Boko Haram suka kai a kauyen Ndongo a kwanakin da suka shude

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.