Ebola

Kasashen Duniya na jan kaffa wajen yakar Ebola

Samantha Power Jakadiyar Amurka  a MDD.
Samantha Power Jakadiyar Amurka a MDD. REUTERS/Eduardo Munoz

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dimkin Duniya Samantha Power tayi mummunar suka ga kasashen duniya kan yadda suka kasa bada gudumawa dan magance cutar ebola a ziyarar da take a kasar Guinea.

Talla

Power tace lokacin da Amurka da Britaniya ke taimakawa kasashen da aka samu barkewar cutar sauran kasashen duniya sun zuba ido.

Cutar kamar dai yada  hukumar lafiya ta duniya ta sanar kusan mutane 5.000 suka mutu daga  cikin 10.000 da suka kamu da ita.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.