Najeriya

Tambuwal ya koma APC

Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Aminu Tambuwal
Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Aminu Tambuwal nigeriansabroadlive.com

Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya Barista Aminu Tambuwal ya fice Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar adawa ta APC, inda ake sa ran zai tsaya takarar gwamna a Jihar Sokoto. An dade ana jita jitar Tambuwal zai fice PDP musamman saboda takun saka tsakanin shi da shugaban kasa Goodluck Jonathan

Talla

A zauren Majalisa ne Tambuwal ya bayyana canza shekar a yau Talata kamar yadda wakilin RFI a Majalisar Aminu Ahmed Manu ya tabbatar.

An dade Tambuwal yana musanta cewa zai fice PDP, kuma a yau bayan bayyana kudirinsa na komawa APC ya rufe Majalisa ya fice.

Tuni dai aka fara cece kuce akan makomar mukamin Tambuwal a Majalisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.